Falasdinwa 11 suka rasa rayukansu a yau Asabar a Gaza saboda yunwa, wanda ya kawo adadin wadanda yunwa ta kasashe a Gaza tun lokacinda HKI ta hana shigowar abinci yankin zuwa 212.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ya nakalto majiyar ma’aikatar kiwon lafiya na Gaza na fadar haka, sannan masana sun bayyana cewa mai yuwa wannan adadin ya wuce haka, saboda ita yunwa tana hana garkuwan jiki aiki, don haka karamin cuta tana iya kashe mutun saboda yunwa. Sun kara da cewa akwai wasu Falasdinawa da dama a wasu wurare a cikin gaza wadanda basa da lafiya amma yunwa ta karasa su a gida ba tare da sun zo asbiti ba.
Larabarin ya kara da cewa a cikin mutane 212 da suka rasa rayukansu 98 daga cikinsu jarirai na wadanda basa iya jurewa yunwa na lokaci mai tsawo.
Shugaban hukumar lafiya ta duniya yayi gargadi a cikin watan yulin da ya gabata kan cewa yunwa zata mullo a gaza saboda hana shigo da abinci wanda HKI take yi.
Shugaban hukumar Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce yara kimani 12,000 yan kasa da shekaru 5 suke fama da yunwa da karancin abinci mai gina jiki.
Wasu masanan sun cewa bayan watanni da hana shigo da abinci a Gaza, mutum guda cikin ko wani mutane uku suna kwana da yunwa a gaza.