Fadan Vatican ta mabiya darikar Katolika ta sanar da mutuwar Paparoma Francis a yau
Fadar Vatican ta bayyana a cikin wata sanarwa ta faifan bidiyo a yau Litinin cewa: Paparoma Francis, shugaban darikar Katolika dan Latin Amurka na farko, ya kawo karshen mulkin da ya yi fama da rikici, rarrabuwar kawuna, da tashin hankali a yayin da yake kokarin kawo sauyi a cibiyoyin majami’u.
Cardinal Kevin Farrell ta hanyar gidan talabijin na Fadar Vatican ya shelanta cewa; Ya ku ‘yan uwa maza da mata masu daraja, tare da bakin ciki da alhini, ina sanar da mutuwar Fafaroma Francis”, da karfe 7:35 na safiyar yau (agogon gida), yana mai jaddada cewa: Francis, ya koma gidan mahaifinsa.”
Fafaroma Francis yana da shekaru 88 a duniya kuma ya sha fama da cututtuka daban-daban a tsawon shekaru 12 da ya yi yana sarauta.