Fadar Mulkin Amurka: Tattaunawa Da Iran Ta Yi Armashi

Fadar mulkin Amurka ta “White Hosue” ta bayyana cewa tattaunawar da aka yi a tsakanin ministan harkokin wajen Iran Abbas Arakci  da wakilin Donald Trump

Fadar mulkin Amurka ta “White Hosue” ta bayyana cewa tattaunawar da aka yi a tsakanin ministan harkokin wajen Iran Abbas Arakci  da wakilin Donald Trump akan gabas ta tsakiya Steve Witkoff, ta hanyar shiga tsakanin kasar Oman, ta yi armashi.

Da marecen jiya Steve Witkoff ya bayyana cewa; shugaba Donald Trump ya ba shi umarnin ya yi duk abinda zai iya domin rage tazarar sabanin da ake da ita ta hanyar tattaunawa da diflomasiyya.

Bayanin na fadar mulkin Amurka ya kuma yaba wa kasar Oman wacce ta kasance mai masaukin baki na tattaunawar da aka yi wacce ba ta gaba da gaba ba ce a tsakanin Amurkan da kuma Iran.

Gabanin bayanin na fadar mulkin Amurkan, manzon musamman na shugaba Donald Trump, Steve Witkoff ya fada wa tashar talabijin din NBC cewa, ya yi tattaunawa mai matukar armashi da kuma amfani.

Tun a ranar Asabar da safe ne dai ministan harkokin wajen na Iran Abbas Arakci ya isa birnin Mascut, inda ya gana da takwaransa na kasar Sayyid Hamad Bin Hamud al-Busa’idi, tare da mika masa bayanai da su ka kunshi mahangar Iran akan tattaunawar.

Ministan na harkokin wajen Oman ya zama mai shiga tsakanin kasashen biyu a tsawon lokacin tattaunawar. Bangarorin biyu sun yi musayar takardu har sau hudu.

A ranar Asabar mai zuwa ne dai za a ci gaba da tattaunawar daga inda aka tsaya a wani wurin da ba a kai ga ayyana shi ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments