Equatorial Guinea ta zargi Faransa da karan-tsaye wa zaman lafiya a kasar

Kasar Equatorial Guinea, ta zargi Faransa da karan tsaye wa zaman lafiya a kasar. mataimakin shugaban kasar Equatorial Guinea Teodoro Nguema Obiang Mangue ya yi

Kasar Equatorial Guinea, ta zargi Faransa da karan tsaye wa zaman lafiya a kasar.

mataimakin shugaban kasar Equatorial Guinea Teodoro Nguema Obiang Mangue ya yi tir da “tsarin Faransa na neman da yunkurin kawo cikas ga zaman lafiya a kasar a wani sakon da ya wallafa a shafin X..

Faransa na goyan bayan ‘yan tada zaune tsaye, ta hanyar tunzura su da su kawo cikas ga zaman lafiya, in ji Mataimakin Shugaban kasar a wani lamari da ba a saba gani ba.

“Mun yi watsi da manufofin tsattsauran ra’ayi da jamhuriyar Faransa ke bi don tada zaune tsaye a kasarmu, kamar yadda ta yi da sauran kasashen Afirka kamar Mali, Nijar, da Burkina Faso, da dai sauransu. A.”

Equatorial Guinea kasa ce da ke magana da harshen Espanya a Afirka ta Tsakiya, mai arzikin mai.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted