A wata tattauna ta wayar tarho, ministocin harkokin wajen kasashen Iran da Masar sun yi dubi kan halin da ake ciki yankin.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da kasashen Masar, Turkiya da kuma Pakistan gami da Oman suke ta kokarin ganin an samu daidaito wanda zai kawo karshen yakin da Amurka da Isra’ila suka kaddamar a kan kasar Iran.
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya tabbatar wa takwaransa na Masar da cewa, basu da wata matsala ga duk wani yunkuri wanda zai kawo karshen yakin baki daya bisa adalci da kuma sharuddan Iran.
sannan kuma ya jadadda cewa kafin cimma duk wata matsaya Iran za ta ci gaba da daukar dukkanin matakan da ta ga sun dace domin kare kanta da al’ummarta.