ECOWAS Za Ta Aika Kwamitin Sulhu Zuwa Kasashen AES

Majalisar Dokokin ECOWAS, ta kafa wani kwamiti na musamman domin tattaunawa da shugabannin kasashen Burkina Faso, Mali, da Nijar da suka fice daga kungiyar, tare

Majalisar Dokokin ECOWAS, ta kafa wani kwamiti na musamman domin tattaunawa da shugabannin kasashen Burkina Faso, Mali, da Nijar da suka fice daga kungiyar, tare da kokarin magance matsalolin siyasa a yankin Yammacin Afirka.

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya, Sanata Barau Jibrin, wanda mamba ne a Majalisar ECOWAS, ya tabbatar da haka a wata tattaunawa da ya yi da manema labarai.

Ya ce an yanke wannan shawara ne bayan wani taro da aka gudanar a Legas.

A cewar Sanata Barau, manufar kwamitin ita ce tattaunawa da shugabannin kasashen AES don fahimtar juna da jaddada muhimmancin ci gaba da kasancewa cikin ECOWAS, musamman idan aka yi la’akari da dangantakar tattalin arziki da zamantakewa da ke tsakanin jama’ar yankin.

Shugabar Majalisar Dokokin ECOWAS, Hadja Memounatou Ibrahima, ta ce kafa kwamitin zai taimaka wajen shawo kan matsalolin siyasa a yankin da kuma hana ƙarin ƙasashen Yammacin Afirka ficewa daga ECOWAS.

A ranar 29 ga watan Janairu, 2025, kasashen Burkina Faso, Mali, da Nijar – waɗanda suka hade a karkashin Kawancen Kasashen Sahel (AES) – sun sanar da ficewarsu daga ECOWAS.

Duk da hakan, ECOWAS ta tabbatar da cewa babu wata matsala a ɓangaren sufuri da kasuwanci tsakanin kungiyar da kasashen AES, domin har yanzu ana ci gaba da hulda tsakanin al’ummomin yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments