Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka ECOWAS ta kaddamar da wata rundinarta mai manufar yaki da ayyukan ta’addanci da miyagun laifuffuka a yankin.
Ministan tsaron Nijeriya, Mohammed Badaru Abubakar ne ya sanar da hakan a yayin taron Kolin ECOWAS na hafsoshin tsaro karo na 43 a babban birnin tarayyar Nijeriya Abuja a ranar Talata.
Badaru ya ce taron ya jaddada kudurinsu na magance matsalolin tsaro da ke addabar yankin.
“Kaddamar da wannan runduna yana kara jaddada kudurinmu na tunkarar ta’addancin da ya shafi tsaron yankin,’’ in ji shi.
Taron ya samu halartar manyan hafsan hafsoshin tsaro na kasashen kungiyar ECOWAS, banda kasashen Mali da Burkina Faso da Nijar wadanda suka raba gari da kungiyar.