Kungiyar ci gaban kasashen yammacin Afirka, ECOWAS ta nuna damuwa kan takun-tsakar da ya kunno kai tsakanin kasar Mali da makwafciyarta Aljeriya, lamarin da ya kai ga kasashen biyu janye jakadu a tsakaninsu.
A cikin wata sanarwa da ta fitar, Ecowas ta ce “Tana bibiyar abin da ke faruwa wanda ya shafi dangantakar da ke tsakanin kasar Mali da kuma Aljeriya.
Ecowas din ta ce ta damu matuka kan lamarin, tana kuma mai kira ga kasashen na Mali da Aljeriya da su kai zuciya nesa, su yi amfani da hanyoyin diflomasiyya wajen warware sabanin ra’ayin da ke a tsakaninsu.”
Dangantaka tsakanin Mali da Aljeriya, ta yi tsami ne bayan da a makon da ya gabata Aljeriya ta kakkabo wani jirgi maras matuki mallakin sojojin kasar Mali, wanda ta ce ya keta iyakar kasarta.
Mali ta mayar da martani ta hanyar yi wa jakadanta da ke Aljeriya kiranye, haka nan ma kasashen kumgiyar yankin Sahel na AES, sun bi sahun Mali ta hanyar daukar irin wannan mataki, Lamarin da ya sanya ita ma Aljeriya ta mayar da martini makamancin wannan ga kasashen.