ECOWAS : Kofarmu A Bude Take Ga Al’ummun Kasashen Burkina, Mali Da Nijar

Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka (ECOWAS) ta ce kofar kasashe mambobinta a bude take domin shige da ficen al’ummun kasashen kawancen Sahel da

Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka (ECOWAS) ta ce kofar kasashe mambobinta a bude take domin shige da ficen al’ummun kasashen kawancen Sahel da suka balle daga cikinta wato Burkina Faso, Mali da Nijar.

A wata sanarwar da ta fitar ranar Laraba a shafinta na X, ECOWAS ta ce duk da cewar daga ranar Laraba 29 ga watan Janairun shekarar 2025 ne ficewar kasashen daga ECOWAS ta tabbata, tana kira ga kasashe mambobinta su saurara wa al’ummmun kasashen uku.

Sanarwar ta ce saboda hadin kai na yankin da amfanin jama’a da kuma shawara da muhukuntan ECOWAS suka yanke ta barin kofar kungiyar a bude, ECOWAS za ta ci gaba da amincewa da fasfo din ‘ya’yan kasashen da ke dauke da tambarin ECOWAS.

Ta kara da cewa ta nemi dukkan ƙasashen ECOWAS su ci gaba da bin tsarin sassaucin kasuwanci bisa shige da fice na kayayyaki da ma’aikata daga kasashen AES zuwa kasashen ECOWAS.

Kazalika ECOWAS ta nemi kasashen su ba da hadin kai ga jami’an ECOWAS daga kasashen a ciki aikin su ga ECOWAS, har zuwa lokacin da shugabannin kasashen ECOWAS za su yanke shawara game da irin huldar da za su yi da kasashen uku.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments