Duniya Na Ci Gaba Da Mayar Wa  Da Donald Trump Martani Akan Gaza

Kasashen larabawa masu kawance da Amurka sun kasance a sahun gaba wajen mayarwa da shugaban kasar Amurkan martani, bayan da ya bayyana cewa kasarsa za

Kasashen larabawa masu kawance da Amurka sun kasance a sahun gaba wajen mayarwa da shugaban kasar Amurkan martani, bayan da ya bayyana cewa kasarsa za ta shimfida ikonta a Gaza, bayan fitar da Falasdinawa da Gaza.

Gabanin wannan sanarwar ta  Shugaba Donald Trump ya bayyana cewa ya tuntubi kasashen Jordan da Masar masu makwabtaka da Falasdinu da su karbi bakuncin mutanen Gaza na wani lokaci har zuwa sa’adda za a gyara wajen.

Masar da Jordan sun yi watsi da wannan shirin da suke dauka a matsayin wata dabara ce ta fitar da Falasdinawa daga cikin kasarsu, da maye gurbinsu da yahudawa ‘yan share wuri zauna.

A wani bayani da kungiyar hadin kan Larabawa ta fitar ta bayyana cewa; Abinda  Trump din ya fada yana da tayar da hankali, kuma yin kira ne ga hargitsa yankin.

Kungiyar mai kasashe mambobi 22 ta kuma kara da cewa, wannan shawara da Trump ya fito da ita, tana cin karo da dokokin kasa da kasa.

Ita ma kungiyar kasashen musulmi ta ( OIC) da take wakiltar musulmin duniya miliyan 1.5, ta ce za ta ki amincewa da wannan shawarar wacce take son sauya tsarin zamantakewa na wannan yankin.

Wasu daga cikin kasashen wannan yankin abokan Amurka da su ka yi watsi da shirin na Trump na  korar Falasdinawa daga Gaza    sun hada Saudiyya, Jordan, Masar, Katar da Hadaddiyar Daular Larabawa, sai kuma Turkiya.

Ita ma MDD ta bayyana cewa hanyar kawo karshen batun Falasdinu shi ne abinda ta kira; Kafa kasashe biyu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments