Gwamnatin Iran ta bayyana cewa duk wata matsin lamba kan kasar ta Donald Trump za ta cutura.
Iran dai ta caccaki matakin da shugaban AMurka ya dauka ind aya sanya hannu kan umurnin sanya sauraren matakn matsin lamba kan Tehran a game da shirinta na nukiliya.
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana a wani sako a X cewa siyasar matsim lamba ta gaza a baya, kuma za ta ci karo da tsayin daka mai karfi.
Abbas Araghchi ya kara da cewa abu ne mai sauki a samu hanyoyin tabbatar da cewa Iran ba ta nemi kera makamin nukiliya ba.
To amma a sa’i daya kuma wajibi ne Amurka da kasashen yammacin duniya su dage takunkumin karya tattalin arziki da suka kakabawa Iran.
Dokar zartarwar da shugaba Trump ya rattabawa hannu na da nufin rage yawan man da Iran take fitarwa zuwa sifili da kuma kakaba ma ta takunkumi mai tsauri, da kuma dakarun kare juyin juya hali, da manyan sojojin kasar.
Har ila yau, ta shafi shirin nan na makamman ballistic na Tehran, da kungiyoyin dake goyan bayan ta a yankin kamar Hizbullah, Hamas da Houthis.
Kasashen Yamma suna zargin Tehran da hanzarta shirinta na nukiliya, musamman ta hanyar inganta sinadarin Uranium zuwa kashi 60 cikin 100, sabanin yarjejeniyar 2015 da manyan kasashen duniya.