Dubban mutanen kasar Moroko ne su ka fito kan titunan birnin Rabat domin yin Zanga-zangar nuna goyon bayansu ga al’ummar Falasdinu da HKI take yi wa kisan kiyashi.
Mahalarta Zanga-zangar sun hada lauyoyi, dalibai, kungiyoyin fararen hula da sauran mutanen gari, suna dauke da tutar Falasdinu, tare da kuma da bayar da taken: “Yanci ga Falasdinu, da yin kira da a shigar da kayan agaji a cikin yankin na Gaza.
Bugu da kari, masu Zanga-zangar sun yi gangami a bakin ginin majalisar dokokin kasar.
Mutanen sun nuna rashin amincewarsu da halin da mutanen Gaza suke ciki, tare da yin kira da a kawo karshensa.
Mahalarta Zanga-zanagr dai sun fito ne daga biranen Tangier, Casbalanca da Feiz, da kuma wasu garuruwa na kasar ta Moroko.
Al’ummar Moroko dai suna cikin masu yawaita Zanga-zanga da gangami domin yin tir da kisan kiyashin da HKI take yi wa mutanen Gaza, da kuma nuna kin amincewa da halin ko’in kula na gwamnatocin kasashen larabawa.