Rahotanni sun bayyana cewa dubun dubatan mutane ne suka gudanar da zanga zangar nuna adawa da kisan kare dangi da Isra’ila ke yi a yankin Gaza, da kuma nuna damuwa game da rawar da birtaniya ke takawa na aikewa da isra’ila makamai, kuma zanga-zangar ta nuna irin tashin hankali da ake ciki game da hakkin yancin walwala da kuma fafututar nuna goyon bayan alummar falasdinu da ake zalunta a birtaniya.
Sama da mutane 500,000 ne daga sassa daban daban na birtaniya suka taru a birnin London domin yin zanga zangar nuna goyon bayan ga alummar Gaza, inda suka fara tun daga dandalin Russell kuma aka kammala a gaban ofishin prime ministen kasar, wanda suka halarci gangami akwai wakilai daga kungiyoyin kishin kasa .
Al Nasarallah wani dan rajin kare hakkin dan adam da ya halarci zanga-zangar yayi gargadi game da yanayi da masu rajin kare hakkin Falasdinawa ke ciki a kasar birtaniya, yace yanayin na kara muni sosai, don haka bisa la’akari da makomar wadannan kungiyoyi ya zama wajibi mu mike tsaye, mu fuskanci gaskiya da adalaci, daga karshe yace demokuradiya da suke Magana akai ba komai ba ce sai cin hanci da rashawa.