Bayan da su ka kwace iko da birnin Goma dake gabashin kasar DRC, kungiyar ‘yan tawaye ta M 23 wacce take samun goyon bayan kasar Rwanda ta sha alwashin kama hanyar shiga babban birnin kasar Kinsasha.
Wani daga shugabannin kungiyar ta M 23, Corneilla Nangaa ya furta cewa,: manufarmu ita ce, muna yin yaki ne saboda kishin Congo, ba muna yaki ne saboda samun ma’adanai ba, babu wani dalili na daban da ya sa muke yaki.”
Da akwai wasu rahotanni da suke nuni da cewa, ‘yan tawayen na M 23 sun kama hanyar zuwa Bukavu, wanda shi ne birni mafi girma na biyu a yankin.
Nangaa ya ce babu wata gwamnati tsayayya a kasar Congo, domin Tshikedi ya riga ya rusa sojoji, ‘yansanda, kuma tsarin tafiyar da mulki, haka nan kuma ma’aikatar shari’a.”
Sai dai kuma ‘yan tawayen sun ce a shriye suke a bude tattaunawa domin a dama da su a cikin sha’anin tafiyar da kasar.
Kungiyoyin kasa da kasa suna yin kira da a tsagaita wutar yaki a kasar ta DRC.