DRC: Kungiyar M23 Ta Kori Fararen Hula Zuwa Kasar Rwanda

Rahotanni daga kasar DRC sun ce  a ranar Litinin din da ta gabata kungiyar ‘yan tawaye ta M23 ta kori fararen hula 181  daga garin

Rahotanni daga kasar DRC sun ce  a ranar Litinin din da ta gabata kungiyar ‘yan tawaye ta M23 ta kori fararen hula 181  daga garin Goma zuwa kasar Rwanda.

Kungiyar ta zargi fararen hular da ta kora da cewa, ba ‘yan kasa ba ne, asalinsu daga kasar Rwanda ne.

Bugu da kari an gabatar da wasu dubban mutane  tare da iyalansu da ake daukar cewa masu laifi ne, da aka zuba su a cikin manyan motoci a yankin Karenga dake yankin Kivu ta arewa.

Mafi yawancin iyalan da aka dauka suna a yankin da yake karkashin ikon kungiyar ‘yan tawaye da Democratic Forces For Liberation of Rwanda       ( FDLR).

Gwamnatin Rwanda da kuma kungiyar M23 suna zargin kungiyar FDLR da cewa, tana tafka laifuka a yankin  da take rike da shi.

Rahotannin sun ambaci cewa, mafi yawancin wadanda aka kora din suna zaune ne a cikin hemomi na ‘yan hijira dake Sake, da ba shi da nisa sosai daga Goma.

Mai Magana da yawun hukumar ‘yan hijira ta MDD, ( UNHCR)  Eujin Byun ta bayyana cewa; an mika mutane 360 zuwa kasar Rwanda a ranar Asabar din da ta gabata.

Ita dai kungiyar M23 wacce ta shimfida ikonta a mafi yawancin yankunan da suke gabashin DRC, tana samun cikakken goyon bayan Rwanda wacce ta aike mata da sojojin da sun kai 4000.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments