DRC : Kinshasa Ta Rufe Sararin Samaniyarta Ga Jiragen Rwanda

Jamhuriyar Demokuradiyyar Kwango ta yanke shawarar rufe sararin samaniyarta ga “dukkan jiragen sama na farar hula ko na gwamnati masu rijista dake zaune a Rwanda”.

Jamhuriyar Demokuradiyyar Kwango ta yanke shawarar rufe sararin samaniyarta ga “dukkan jiragen sama na farar hula ko na gwamnati masu rijista dake zaune a Rwanda”.

A cewar Kamfanin Dillancin Labarai na Kwango, matakin ya “hana shawagi da sauka a cikin kasar ta Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango, saboda dalilai na rashin tsaro da ke da nasaba da rikicin masu dauke da makamai.”

A taswirorin zirga-zirgar jiragen sama na duniya, jiragen sama daga Kigali na kasar Rwanda, yanzu haka na kaucewa shiga sararin samaniyar Kongo.

Bayanai sun ce wani jirgin da ya tashi daga babban birnin kasar Rwanda zuwa birnin Landan na kasar Birtaniyaa ranar Talata, an tilas ya sauya hanyarsa don yin aiki da dokar, wanda a yanzu ya shafi “dukkan jiragen da suka yi rajista ko kuma suna zaune a Rwanda.”

A ranar Laraba, ma wasu jiragen Rwandair daga Kigali zuwa Libreville, Gabon, ko Lagos, Nigeria, suma sun yi zagaye don gujewa sararin samaniyar Kongo, lamarin daya shafi matafiya zuwa Libreville, da Najeriya wadanda suka samu karin sa’o’i uku na tafiya.

Ga kamfanonin da abin ya shafa, kuwa dokar zata tilasta musu karin kudin man fetur.

DR Kwango da Rwanda dai na takun tsaka game da rikin ‘yan tawayen M23 da Kinshassa ke zargin Kigali da goyan baya a rikicin gabashin kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments