Rahotanni daga kasar ta DRC sun ambaci cewa an ga tsohon shugaban kasar Joseph Kabila a jiya Alhamis a garin Goma wanda yake a karkashin ikon ‘yan tawayen kungiyar M23.
Majiyar malaman addinin kirista a yankin ce ta sanar da cewa, ta gayyace shi ne domin ya shiga Tsakani a kawo karshen yakin da ake yi a yankin.
Bishop Joel Amurani ne ya sanar da cewa, su ne su ka gayyaci tsohon shugaban kasar wanda ya kasance akan karagar Mulki daga 2001 zuwa 2019.
A yayin ziyarar tashi a garin na Goma, Kabila ya gana da bangarori mabanbanta da su ka hada da malaman addinin yankin.
A can birnin Kinshasha, gwamnatin Felix Tshisekedi tana zargin Kabila da cewa yana goyon bayan kungiyar ta M23 wacce ta shimfida ikonta a gabashin kasar.