DRC: An Kulla Yarjejeniyar Zaman Lafiya A Tsakanin Gwamnati Da Kungiyar M23

Gwamnatin kasar ta DRC da kuma kungiyar ‘yan tawaye ta M23 sun rattaba hannu akan wasu takardu da su ka kunshi yadda za a kai

Gwamnatin kasar ta DRC da kuma kungiyar ‘yan tawaye ta M23 sun rattaba hannu akan wasu takardu da su ka kunshi yadda za a kai ga samun zaman lafiya mai dorewa a gabashin kasar.

A jiya Asabar ne dai bangarorin biyu su ka rattaba hannu akan  takardun a birnin Doha na kasar Qatar domin kawo karshe fadace-fadacen da ake yi a gabashin kasar da ya ci rayukan dubban mutane da kuma tilastawa wasu yin hijira a cikin shekara daya kacal.

Karamin ministan harkokin wajen kasar Katar Muhammad Bin Abdulaziz Al-Khulaifi ya ce, rattaba hannu da bangarorin biyu su ka yi share fage ne zuwa ga zaman lafiya.

Haka nan kuma ya ce; Shi zaman lafiya ba a iya tilasta shi ta hanyar amfani da karfi,sai dai ta fahimtar juna.”

Sai dai kuma duk da cewa ana tattaunawar zaman lafiya a tsakanin banbarorin biyu a kasar Katar, fadan da ake yi a can gabashin DRC bai tsaya baki daya ba. A ranar juma’ar nan da ta shude ma dai an kashe mutane 28 a wani hari da kungiya mai ikirarin jihadi ta kai a Kivu ta Arewa.

A cikin watan Janairu na wannan shekarar ne dai kungiyar ta M23 ta shimfida ikonta a cikin birnin Goma da shi ne mafi girma a gabashin kasar, daga can kuma ta kame yankunan Kivu ta Arewa da ta kudu.

Gwamnatin Kinshasha dai tana tuhumar makwabciyarta Rwanda da taimakawa kungiyar ta M23 da makamai da kuma mayaka. Sai dai Rwanda ta sha musanta zargin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments