Dr. Larijani: Iran Tana  Kan Ganiyar Shirin  Mayar Wa Da HKI Martani

Mai bai wa jagoran juyin musulunci na Iran shawara, ya bayyana cewa; Iran tana kan ganiyar shirin mayar wa da Isra’ila martani. A wata hira

Mai bai wa jagoran juyin musulunci na Iran shawara, ya bayyana cewa; Iran tana kan ganiyar shirin mayar wa da Isra’ila martani.

A wata hira da kamfanin dillancin labarun “Tasnim” na Iran ya yi da Dr. Ali Larijani, ya bayyana cewa; A halin yanzu sojoji suna kan ganiyar shirya martanin da za su mayarwa da ‘yan mamaya.

Dr. Ali Larijani ya yi ishara da ziyarar da ya kai zuwa kasar Lebanon kwanakin da su ka gabata, yana mai cewa, ya ga karfin da Hizbullah take da shi, kuma yanzu kungiyar ce take kera makamai masu linzami da kanta.

Haka nan kuma Dr. Larijani ya ce a daren da Sayyid Hassan Nasrallah ya yi shahada, mayakan Hizbullah sun yi rantsu za su fuskanci HKI har zuwa karshe.

Dangane da batun rusa karfin Hizbullah da HKI ta riya cewa ta yi, Dr. Ali Larijani ya ce; Makaman da Hizbullah take harbawa a yanzu ina suke zuwa?

Da kuma aka yi masa tambaya akan batun tattaunawa a tsakanin Iran da yammacin turai, Dr. Ali Larijani ya ce, Idan har ba su zauna akan teburin tattaunawa ba,  kuma ba su yarda da sharuddanmu ba, to tattaunawar ba ta da wani muhimmanci.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments