Sharhin bayan labaran namu zai yi magana ne kan kiran da tsohon shugaban kasar Amurka kuma dan takarar shugabancin a halin yanzu Donald Trump ya yi ga gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila kan kai hari kan cibiyoyin makamashin nukiliyar Iran, yayin da shugaban kasar ta Amurka mai ci Joe Biden ya nuna adawarsa ga duk wani kai harin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila kan cibiyoyin nukiliyar kasar ta Iran, da ni Sunusi Wunti zan jagoranci gabatar muku da Shirin:-
Tsohon shugaban Amurka kuma dan takarar jam’iyyar Republican a zabe mai zuwa, Donald Trump, ya ce dole ne gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta kai hari kan cibiyoyin nukiliyar kasar Iran.
Da yake magana a jihar Arewacin Carolina, Trump ya yi ishara da tambayar da aka yi wa shugaba Joe Biden a tsakiyar mako game da yiwuwar gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta kai hari kan cibiyoyin nukiliyar Iran. Trump ya ce, “Sun gabatar da wannan tambaya ce, kuma ya kamata amsar da kasance goyon bayan kai harin, sannan a kula da sauran abin da zai biyo baya.
A ranar Larabar da ta gabata, Biden ya bayyana rashin amincewarsa da kaddamar da hare-haren haramtacciyar kasar Isra’ila kan cibiyoyin nukiliyar Iran, kwana guda bayan Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta harba makamai masu linzami kimanin 200 a kan haramtacciyar kasar Isra’ila, a wani harin da Iran ta ce ya zo ne a matsayin martani ga kisan gillar da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta yi wa babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon, Sayyid Hassan Nasrallah, da kuma shugaban ofishin siyasa na kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas Isma’il Haniyyah.
Biden ya fadawa manema labarai yayin da yake amsa wata tambaya game da yiwuwar goyan bayansa ga irin wannan yunkuri na haramtacciyar kasar Isra’ila: inda ya amsa da cewa: A’a baya goyon bayan wannan kasada. Ya kara da cewa: “Su bakwai sun yarda cewa gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila tana da ‘yancin mayar da martani, amma dole ne ta mayar da martani daidai gwargwadon da ta dace,”.
Har yanzu haka dai Trump ya yi shiru game da tashe-tashen hankula na baya-bayan nan a yankin Gabas ta Tsakiya, inda ya takaita da fitar da wata sanarwa a farkon wannan mako da dora wa Joe Biden da mataimakiyarsa Kamala Harris alhakin barkewar tashe-tashen hankulan.
Shugaban kasar Amurka Joe Biden dai ya ce: Ba ya goyon bayan kaddamar da hari kan cibiyoyin nukiliyar kasar Iran biyo bayan harin mayar da martani da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta kai wa haramtacciyar kasar Isra’ila, yayin da fadar shugabancin White House ta ce kungiyar kasashe bakwai ta G7 masu karfin tattalin arziki a duniya tana tunanin kakabawa kasar Iran takunkumi, kuma kungiyar ta G7 ta yi kira da a rage tashe-tashen hankala a yankin Gabas ta Tsakiya.
Biden ya shaida wa manema labarai cewa: Za su tattauna da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila kan abin da za su yi, amma dukkanin kasashen G7 sun yarda cewa; Haramtacciyar kasar Isra’ila tana da ‘yancin mayar da martani, amma dole ne ya kasance daidai da irin barnar da aka mata.
Biden ya kara da cewa: Za su kakabawa kasar Iran karin takunkumai da ke nuni da cewa nan ba da jimawa ba zai yi magana da fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu.
Fadar White House ta sanar a cikin wata sanarwa a ranar Laraba cewa: Kungiyar G7 ta yi Allah wadai da harin da kasar Iran ta kai kan haramtacciyar kasar Isra’ila, kuma tana tunanin sanyawa Iran din sabbin takunkumai.
Sanarwar ta ce: Shugaba Joe Biden ya halarci tattaunawa ta wayar tarho da shugabannin kungiyar G7 “don tattauna hare-haren da kasar Iran ta kai kan haramtacciyar kasar Isra’ila wanda ba abu ne da za a amince da shi, da kuma samun daidaiton baki kan mayar da martani gami da kakaba sabbin takunkumai.”
A cikin wannan yanayi, Amurka ta gargadi Iran a kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya game da kai mata hari ko kai wa haramtacciyar kasar Isra’ila hari.
Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Linda Thomas-Greenfield ta shaida wa kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya cewa: Hakkinsu shi ne kare kai, ta kara da cewa: Gwamnatin Iran za ta dauki alhakin duk abin da za ta aikata, kuma suna yin gargadi da kakkausar murya kan kasar Iran ko kawayenta da su guji daukan wani mataki kan Amurka, ko kuma duk wani mataki kan haramtacciyar kasar Isra’ila.
Jakadiyar ta Amurka ya ci gaba da cewa: Dole ne kwamitin sulhu ya yi Allah wadai da harin na Iran tare da dorawa dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran alhakin duk wani mummunan sakamako da zai biyo baya.