Doha: Manya-Manyan Jami’an Hamas Sun Gana Da Aragchi A Doha

Shugaban kungiyar Hamas Khalil Al-Hayya da kuma wasu manya-manyan shuwagabannin kungiyar Hamas a Gaza, sun gana da ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas arachi a

Shugaban kungiyar Hamas Khalil Al-Hayya da kuma wasu manya-manyan shuwagabannin kungiyar Hamas a Gaza, sun gana da ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas arachi a yau a birnin Doha na kasar Qatar.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa wannan haduwar itace ta farko tun bayan yakin kwanaki 12 kan kasar Iran wanda HKI tayi, wanda kuma yake nuna irin yadda gwamnatin JMI ta damu a al-amarin Falasdinawa.

A baya-bayan dai kasashen duniya da dama sun bayyana anniyarsu ta bayyana goyon bayansu ga kafa kasar falasdinu mai cikekken yanci, mai kuam zaman kanta a babban taron shuwagabanni kasashen duniya a babban zauren majalisar dinkin duniya a cikin wannan watan da muke ciki. Daga cika har da wasu manya-manyan kasashen Turai.

Amma ga Amurka da HKI kuma, taron Aragchi da Jami’an Hamas yana nuna cewa har yanzun kasar Iran tana nan daram a goyon bayan da takewa al-ummar Falasdinu. Musamman wadanda suke birnin gaza, wadanda HKI take son korarrsu.

Taronda ya maida hankali kan sabbin labarai dangane da falasdinu da kuma kan abinda yake faruwa a gaza.

Aragchi ya bayyana cewa Iran zata ci gaba da kasancewa tare da falasdinawa har zuwa lokacinda zasu sami dukkan hakkokinta.

Ya ce, abubuwan da suke faruwa a duniya na zanga-zanga da yin All..wadai da kuma hanyoyoyin daban daban na nuna rashin amincewa da abinda HKI take a kasar Falasdinu alama ce ta farkawar mutane kan hakikanin HKI.

Al-Hayya shugaban Hamas ya gabatar da rahoto kan halin da ake ciki a gaza, da kuma kiran a tada kayar baya kan Amurka da HKI don kawo karshen kisan kiyashi na gaza, da kuma bude kofofin gaza don shigo da abinci.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments