Dembele Ya Lashe Kyautar Ballon d’Or Ta Shekara Ta 2025.

An bayyana dan wasan a matsayin wanda ya lashe kyautar ne a bikin da aka gudanar ranar Litinin 22 ga watan Satumban 2025 a dakin

An bayyana dan wasan a matsayin wanda ya lashe kyautar ne a bikin da aka gudanar ranar Litinin 22 ga watan Satumban 2025 a dakin taro na Theatre du Chatelet da ke birnin Paris a kasar Faransa.

Ballon d’Or kyauta ce da akan bai wa dan wasan da ya nuna gwaninta a kowace shekara, inda akan yi la’akari da gudunmawar da dan wasan ya bayar ga kungiya da kuma kasarsa.

Tun farko an fitar da jerin ‘ƴan wasa 30 cikin wadanda ake sa ran za su lashe kyautar.

Dembele ya taka rawar gani wajen taimakon kungiyar PSG ta lashe gasar Ligue 1 da da kuma samun nasarar lashe gasar Champions Leage na farko a tarihinta, sannan ta kai wasan karshe a gasar kofin duniya ta ƙungiyoyi.

Ya zura ƙwallo 21 a wasa 29 da ya buga a gasar Ligue 1, inda ya karkare gasar a matayin wanda ya fi zura kwallo, sannan ya lashe kyautar gwarzon dan’wasan gasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments