Daruruwan ‘Yan Share Wuri Zauna Sun Kutsa Masallacin Kudus

A jiya Litinin daruruwan yahudawa ‘yan share wuri zauna sun kutsa cikin masallacin kudus, suna masu bayar da take na tsokana ga Musulmi. Har ila

A jiya Litinin daruruwan yahudawa ‘yan share wuri zauna sun kutsa cikin masallacin kudus, suna masu bayar da take na tsokana ga Musulmi. Har ila yau ‘yan share wuri zauna din sun kuma gudanar da na’u’oin ibadu na addinin yahudanci a cikin farfajiyar masallacin na Kudus.

Ma’aikatar  da take kula da wuraren ‘wakafi’ na musulunci, ta bayyana cewa; Adadin yahudawa ‘yan share wuri zauna din da su ka kutsa cikin masallacin na Kudus sun kai 765,kuma ‘yan sanda sun rika yi musu rakiya.

A lokaci daya kuma jami’an tsaron na ‘yan sahayoniya sun tsaurara matakan kuntatawa Falasdinawa masu shiga cikin masallacin na Kudus domin yin salla.

Wannan tsokanar ta ‘yan share wuri zauna a masallacin Kudus, tana faruwa ne a lokacin da a can yammacin kogin Jordan, yahudawan suke lalata gonakin Falasdinawa da kankare kasar gonakin ta hanyar amfani da manyan motoci na buldoza.

Har ila yau ‘yan sandan HKI sun kutsa cikin garuruwa da dama na Falasdinawa a yammacin kogin Jordan, inda su ka kama mutane da dama. Haka nan kuma sanadiyyar  harbe-harebn da su  ka yi, sun jikkata Falasdinawa 4 a sansanin Jalzuna dake arewacin birnin Ramallah.

A birnin Tubas kuwa ‘yan sahayoniyar sun kutsa cikin unguwanni mabanbanta tare da tilastawa mazauna wasu unguwanni da su fice daga cikin gidajensu. Kwamitin al’umma na Falasdinu a yankin ya sanar da cewa  a tsawon lokacin yaki adadin Falasdinawan da aka tilastawa ficewa daga cikin gidajensu, sun kai dubu 3 da 227.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments