Dangote zai sayar da kaso 10 na hannun jarin matatar man shi

Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya ce matatar man shi na shirin sayar da tsakanin kashi 5 zuwa 10 cikin 100 na hannun

Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya ce matatar man shi na shirin sayar da tsakanin kashi 5 zuwa 10 cikin 100 na hannun jarinta a kasuwar hannun jari ta Najeriya.

Ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da S&P Global, inda ya ce ana sa ran sayar da hannun jarin a cikin shekara mai zuwa.

Dangote ya ce wannan mataki kwatankwacin irin yadda aka gudanar sayar da hannun jarin kamfanononin siminta da suga na Dangote ne. “Ba ma son mu riƙe fiye da kashi 65 zuwa 70 cikin 100,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa za a sayar da hannun jarin a hankali, gwargwadon sha’awar masu zuba jari da ƙarfin kasuwa.

Hamshakin dan kasuwar ya ce kamfanin na duba yiwuwar hadin gwiwa da kamfanonin Gabas ta Tsakiya domin tallafa wa fadada  matatar da kuma habaka sabon aikin sinadarai a kasar China.

Dangote ya ce Kamfanin Man Fetur na kasa (NNPC) Limited na iya kara hannun jarinsa a matatar bayan rage shi zuwa kashi 7.2%.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments