Dangantaka Na Kara Tsami Tsakani Faransa Da Isra’ila Kan Falasdinu .

Matsayar kasar Faransa na amincewa da Falasdinu a matsayin kasa a hukumance a babban taron zauren majalisar dinkin duniya dake zuwa,  ya kawo tarnaki sosai

Matsayar kasar Faransa na amincewa da Falasdinu a matsayin kasa a hukumance a babban taron zauren majalisar dinkin duniya dake zuwa,  ya kawo tarnaki sosai a alakar diplomasiya tsakanin ta isara’ila.

Shugaban kasar faransa Emmanuel Macron ya sanar tun a watan yuli cewa faransa za ta amince da falasdinu a matsayin kasa, za ta shiga cikin jerin kasashe da ke goyon bayan kafa kasashe biyu masu yancin kai.

Ana sa bangaren ministan harkokin wajen Isra’ila Gidion Saar ya gargadi Macron da cewa ba’a maraba da shi a Isra’ila har sai faransa ta canza shirinta na amincewa da falasdinu ,yace wannan shirin zai cutar da tsaron Isra’ila kai tsaye.

Shi ma wani babban jami’in  tarayyar turai yayi gargadin cewa alaka tsakanin faransa da isara’ila tana kara tabarbarewa sosai, kuma ana kallon Macron a matsayin kanwa uwar gami.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted