Dan wasan Taekwando Na kasar Iran Ya Samua Lambar Yabo Ta Zinariya

Dan wasan taekwando na kasar iran  Abolfazl zandi ya samu lambar yazo ta zinariya a ranar farko ta gasar takwando ta duniya  da ake gudanarwa

Dan wasan taekwando na kasar iran  Abolfazl zandi ya samu lambar yazo ta zinariya a ranar farko ta gasar takwando ta duniya  da ake gudanarwa a birnin Nairobi na kasar kenya , kuma ita ce lambar yabonsa na biyu a cikin kwanaki 35,

Gasar tana gudana ne a filin wasa na moi international sport center dake kasar kenya kimanin yan wasa 452 da suka fito daga kasashen duniya 75 ne ke halartar gasar, kuma iran ta shiga gasar da yan wasa guda 16 da suka hada da mata 6 da kuma maza 8 da za su yi tasu karawar acikin kwanaki 4.

Zandi da ya samu lambar yabo ta zinairiya a baya –bayan nan ya nuna gwaninta da ya cancanci yabo a bangaren maza masu nauyin kilograme 58.

Bayan zayen farko yayi nasara kan abokin hamayyarsa na kasar Ecodo da kuma meziko kafin ya kai ga matakin kusa da gab da na karshe, kana kuma yayi galaba kan dan kasar brazil ya wuce matakin karshe wato final inda ya doki abokin karawarsa dan rasha, a zagaye biyu da hakan ya bashi damar dauke lambar yabon ta zinariya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted