Sudan Ta Yi Watsi Da Batun Dakatar Da Bude Wuta Da Amurka Ta Gabatar

Rahotanni sun bayyana cewa dakarun sojin kasar Sudan sun yi watsi da bukatar da kasar Amurka ta gabatar mata na dakatar da bude wuta, ta

Rahotanni sun bayyana cewa dakarun sojin kasar Sudan sun yi watsi da bukatar da kasar Amurka ta gabatar mata na dakatar da bude wuta, ta sha alwashin  murkushe dakarun RSF wato kungiyar sojin sa kai ta kasar dake iko da mafiyawancin yankunan yammacin kasar Sudan

Wannan matakin yazo ne bayan taron gaggawa Da majalisar tsaron kasar ta gudanar wanda shugaban majalisar sojojin kasar janar Abdel fatah Al-burhan ya jagoranta inda suka sha alwashin murkushe dakarun kungiyar ta RSF.

Alburhan yayi alkawarin samun nasara yace wadanda suke yaki don kare hakkin alummarsu ba zaa yi nasara akan su ba,

Wadannan bayanan sun zo ne kwanaki kadan bayan da kungiyar ta RSF ta kwace garin al-fasher dake yammacin Darfur inda rahotanni suka bayyana irin kisan kare dangi da tayi da ya tilastawa fararen hula yin gudun hijira zuwa arewaci da kudancin Darfur.

Daga lokacin da yaki ya barke a watan Aprilun shekara ta 2023 tsakanin dakkarun kasar da dakarun kungiyar RSF an kashe dubban mutane kuma akalla mutane miliyan 13 ne suka tarwaste inda kungiyar RSF ke iko da jihohi 5 dake yankin Dafur

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted