Dakarun Izzuddin Qassim a zirin gaza sun bada sanarwan halaka akalla sojojin yahudawan Sahyoniyya 2 a garin Rafah dake kudancin Gaza a yau Jumma’a.
Tashar talabijin ta Almayadin ta kasar Lebanon ta bayyana cewa, dakarun Qassam sun aiwatar da ayyukan soje masu yawa a lokaci guda a garin Rafah kan sojojin yahuwan.
Inda da farko sun bude wuta kan taron sojojin yawahuwan, inda wasu daga cikinsu suka halaka.
Sannan a lokacinda wata tankar yaki samfurin mirkava ta kawo masu dauki, a nan ma dakarun Qassam suka tarwatsata da makami mai suna yasin 105, wannan ya sa wuta ta mamaye wurin, sannan wata motar booldoza ta sojoji ta kawo masu dauki ita ma suka wargazata da makami samfurin yasin 105.
Daga karshen yahudawan sun yi gangami suka yi ta bude wuta ta ko ina, kafin wani jirgin helkobta ya zo ya kwace gawaki da kuma wadanda suka ji rauni.
Banda haka falasdiwan sun ci gaba da fafatawa da sojojin yahuwan a wurare da dama a zirin na gaza.