Search
Close this search box.

Dakarun Kassam Sun Yi Wa HKi Busharar Kai Mata Hare-haren Kunar Bakin Wake

A wani sako da dakarun “Izzuddin –al-kassam” ta fitar a jiya Laraba, ta bayyana cewa; Ba da jimawa ba za ta bude kai hare-haren kunar

A wani sako da dakarun “Izzuddin –al-kassam” ta fitar a jiya Laraba, ta bayyana cewa; Ba da jimawa ba za ta bude kai hare-haren kunar bakin wake a HKI.

Wannan sanarwar dai ta zo ne bayan karanta wasiyyar shahida biyu na dakarun Kassam da su ka kai harin kunar bakin wake a birnin Tel-Aviv.

Shahidi na farko shi ne Ja’afar Muna Sa’ad, da a ciki ya bayyana cewa, garwashin gwgawarmaya ba zai taba mutuwa ba har sai mun kori ‘yan mamaya daga kasarmu da gidajenmu.”

Shahidin ya kuma  fada wa ‘yan shahayoniya cewa; “Wutar yakin da ku ka kunna za ta kone ku, ta kuma zamar muku bala’i, ku da fursunoninku da kuma sojojinku.”

Shahidi na biyu wanda ba a bayyana sunanshi ba, ya bayyana cewa: Gwargwadon yadda kuke kare aikata laifukan yaki akan al’ummarmu da iyalanmu, kuke kara cin bashin jini da daukar fansa, domin bashin jini ba a biyanshi sai da jini.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments