Dakarun Kai Daukin Gaggawar Kasar Sudan Sun Kai Hari Kan Birnin El Fasher Da Ke Darfur

Dakarun Kai Daukin Gaggawa ta kasar Sudan sun kai hare-hare kan sansanin Abu Shouk da ke birnin El Fasher da manyan bindigogi Majiyar sojojin Sudan

Dakarun Kai Daukin Gaggawa ta kasar Sudan sun kai hare-hare kan sansanin Abu Shouk da ke birnin El Fasher da manyan bindigogi

Majiyar sojojin Sudan ta shaidawa gidan talabijin na Al Jazeera cewa, dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces (RSF) sun yi luguden wuta kan sansanin ‘yan gudun hijira na Abu Shouk da ke El Fasher, babban birnin arewacin Darfur a ranar Litinin.

Haka zalika majiyoyin ba su bayar da alkaluman hasarar dukiya ko hasarar rayukan mutane da aka yi a sansanin ba, wanda mazauna sansanin ke fama da matsananciyar rayuwa.

Ofishin kai daukin gaggawa na sansanin ya tabbatar da cewa: Mazauna yankin na fama da karancin abinci, magunguna, da ruwa, wanda hakan ke shafar lafiyarsu da mayar da yara zuwa “kwarangwal”.

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta sansanin ta kara da cewa a shafinta na Facebook, mazauna sansanin ba sa iya barin sansanin ko kuma El Fasher zuwa wasu yankunan saboda rashin tsaro a wuraren da ake fita.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted