Dakarun Izzuddeen-Al-Qassam Suna Ci Gaba Da Tarwatsa Sojojin Yahudawan Sahayoniyya A Rafah

Dakarun Izzuddeen-Al-Qassam suna ci gaba da janyo hasara ga sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila a birnin Rafah ‘Yan gwagwarmayar Falasdinawa suna ci gaba da fuskantar

Dakarun Izzuddeen-Al-Qassam suna ci gaba da janyo hasara ga sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila a birnin Rafah

‘Yan gwagwarmayar Falasdinawa suna ci gaba da fuskantar sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila musamman a garin Jabaliya da kuma gabashin Rafah, inda suke ci gaba da janyo hasarar rayukan sojojin yahudawan sahayoniyya da tarwatsa motocin yakinsu da suke kutsawa cikin yankunan na Falasdinawa.

Rahotonni sun bayyana cewa: Sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila 15 ne suka fada tarkon dakarun Izzuddeen- Al-Qassam bangaren sojin kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas, bayan da wasu ‘yan gwagwarmaya suka ritsa da sojojin yahudawan sahayoniyya a cikin wani gida a Rafah, inda bangarorin biyu suka yi arangama a tsakaninsu da manyan bindigogi da kuma bama-baman hannu  lamarin ya kai ga halakar sojojin na yahudawan sahayoniyya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments