Dakarun kare juyin juya halin musulunci a nan Iran sun yi musayar wuta da yan ta’adda a kudu masu gabacin kasar, sannan wasu daga cikinsu su sun yi shahada sannan sun halaka yan ta’adda da dama.
Kamfanin dillancin labaran Tasnim na JMI ya dakarun na IRGC guda uku nesuka yi shahada a wannan fafatawar, a jiya Laraba a garinLar da ke kusa da birnin Zahidan babban birnin Lardin.
Garin Lar dai yana kan iyakar kasar Iran da Pakisatan, kuma ba wannan ne karon farko wadanda dakarun suke fafatawa da yan ta’adda wadanda suke samun goyon bayan kasashen waje ba. Kuma suke da sansanoninsu a cikin lardin sitan Baluchistan na kasar Pakistan ba.
Har yanzun dakarun rundunar Qudus wanda suke aiki a karkashinsu basu bayyana sunayen sojojin da suka yi shahadar ba. Amma sun kaddamarda wata tawaga wacce zata gudanar da binciken gaggawa don gano abinda ya faru.