Dakarun yaki da ta’addanci na kasar Iraqi sun bayyana cewa sun yi alkwarin yaki tare da kasar iran idan Amurka da HKI suka sake kaddamar da hare- hare kan kasar iran , hakazalika sakatare janar din kungiyar kata’ib sayyidu shuhada abu ala al walai ya ce idan kasar iran ta fuskanci barazana to ko shakka babu zamu shiga cikin yakin kai tsaye.
Walai ya kara da cewa dangantakar dake tsakanin bangarorin yan gwagwarmaya da birnin Tehran ya ketare iyakar alaka ta siyasa, domin dangantakarmu da iran ta tarihi ce da addini, kuma muna daukar iran a amatsayin makwabciya kuma abokiya, ta taimaka mana sosai a lokacin yaki da kungiyar Daesh, ta bangarori daban- daban
Anasa bangaren Brigadiya Janar mohammad Reza Naqbi mai bawa kwamandan dakarun kare juyin musulunci shawara yayi gargadin cewa duk wani yunkurin da amurka za ta yi wajen shigo da sojoji iran ta kasa to zai haifar da mummunan asara ga sojojin Amurka.
Daga karshe Naqdi yayi gargadin cewa shigar sojojin amurka ta kasa zai haifar da mummunan asarar rayuka masu yawa tare da kama sojoji da dama lamarin zai sa amurka ta biya farashi mafi tsada.