Daesh ta yi ikirarin kai hari kan gwamnatin Syria

Kungiyar ‘yan ta’adda ta Daesh ta dauki alhakin kai hari kan dakarun gwamnatin Hayat Tahrir al-Sham (HTC) na kasar Siriya, wanda shi ne irinsa na

Kungiyar ‘yan ta’adda ta Daesh ta dauki alhakin kai hari kan dakarun gwamnatin Hayat Tahrir al-Sham (HTC) na kasar Siriya, wanda shi ne irinsa na farko a kan tsoffin kawayenta tun bayan hambarar da gwamnatin Bashar al-Assad na Siriya.

A wata sanarwa da ta fitar kungiyar ta ce ta sanya “bama-bamai” kan motar dakarun da HTC ke jagoranta a lardin Suwayda da ke kudancin kasar.

Wannan dai shi ne harin farko da Daesh ta yi ikirarin doka kan sabuwar gwamnatin ta Siriya.

Kungiyar kare hakkin dan adam ta Syrian Observatory for Human Rights (SOHR) ta bayar da rahoton cewa, a yayin harin, wasu mambobi uku na runduna ta 70 na rundunar HTC sun jikkata, a yayin da suke sintiri yayin da wata nakiya da aka tayar daga nesa ta tashi a ranar Laraba.

An kuma kashe wani mutum da ke tare da wadannan sojoji a yankin hamadar da ke kewaye.

Shi dai shugaban Syria na yanzu Abu Mohammed al-Jolani tsohon jigo ne a kungiyar Al-Qaeda da Daesh.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments