Ma’aikatar ma’adinai a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo ta sanar da tsawaita dokar hana fataucin ma’adinai na tsawon watanni shida daga wuraren hakar ma’adinai da dama a lardunan Kivu ta arewa da ta kudu da ke fama da rikici.
Sabunta haramcin zai kara kawo tsaiko da cikas wajen samar da wasu ma’adanai a duniya, musamman ma’adaanai irin su tin, tantalum, da tungsten, mahimman abubuwan da ake amfani da su wajen kera kayan lantarki, motoci, da wasu ayyuka na sararin samaniya.
Haramcin, wanda aka fara aiki da shi a watan Fabrairu, ya ci gaba da aiki na tsawon wannan lokaci, inda shaidun ke nuna cewa kayayyakin da ake amfani da su ba bisa ka’ida ba daga ma’adinan suna tallafawa kungiyoyin masu dauke da makamai a gabashin Congo, a cewar wani bayani mai kwanan wata 3 ga watan Nuwamba mai dauke da sa hannun ministan ma’adinai na kasar, Louis Watom Kampaba.
Bayanin ya kunshi shafuka 38 da ke nuni da cewa haramcin ya shafi abubuwa da dama daga ciki har da coltan, cassiterite, da wolframite, tin, tantalum, da tungsten.
Har ila yau kungiyar ‘yan tawayen M23 da sauran kungiyoyi masu dauke da makamai sun kwace filaye da dama a gabashin Kongo mai arzikin ma’adinai a cewar Ministan.
Matakin da ma’aikatar ma’adinai ta dauka ya haramta fitar da kayayyaki daga wuraren hakar ma’adinan da ake magana a kai, kuma ta ce za su iya fuskantar bincike mai zaman kansa daga ma’aikatar ko hukumomin kasa da kasa, ciki har da Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar hadin kan tattalin arziki da raya kasashen yankin gabashin nahiyar Afirka.