Cinikin Kasashen Waje na Iran Ya Zarce Dala Biliyan 76.5

Cinikin kasashen waje na kasar Iran a cikin watanni takwas na farko na bana ya kai tan 131,540, wanda darajarsa ta kai dala biliyan 76.5.

Cinikin kasashen waje na kasar Iran a cikin watanni takwas na farko na bana ya kai tan 131,540, wanda darajarsa ta kai dala biliyan 76.5. kwatankwacin tagomashi na kashi 1.53% idan aka kwatanta da bara warhaka.

Bayanin da aka samu daga hukumar kwastam ta Iran ya ce: “A wannan lokacin, an fitar da tan 105,231,000 na kayayyaki daban-daban, wadanda darajarsu ta kai dala biliyan 37, zuwa kasashe daban-daban.

Wannan adadi yana wakiltar karuwar kashi 1.17% idan aka kwatanta da wannan lokacin a shekarar da ta gabata.

A daya bangaren kuma ” Iran ta kara fitar da kayayyaki zuwa ga Kungiyar Tattalin Arziki ta Eurasia (EAEU), kimanin shekaru biyu bayan yarjejeniyar cinikayyar ‘yanci da aka sanya wa hannu tsakanin Tehran da kungiyar ta fara aiki a watan Disamba na 2023, a cewar sabbin bayanai daga Hukumar Kwastam ta Iran (IRICA).

A cewar alkaluman da aka fitar a ranar Asabar, fitar da kayayyaki daga Iran zuwa ga Kungiyar Tattalin Arziki ta Eurasia wadda Rasha ke jagoranta ya kai dala biliyan 1.46 a cikin watanni takwas da suka wuce a ranar 21 ga Nuwamba, 2025, wanda ya nuna karuwar kashi 11% idan aka kwatanta da wannan lokacin a bara.

 Yawan kayayyakin da aka fitar shi ma ya karu da kashi 10%, inda ya kai tan biliyan 3.888 a wannan lokacin.

Jigilar kayayyaki zuwa Rasha ta karu da kashi 12% a darajar kayayyaki da kuma kashi 9% a girman kayayyaki, yayin da fitar da kayayyaki zuwa Belarus ya karu da fiye da kashi 50% tsakanin Afrilu da Nuwamba, a cewar wannan bayanai.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments