Cin Zarafin Musulmi Na Dada Karuwa A Jamus

A Jamus, kyamar Musulmi na dada karuwa a kasar. A wani rahoto da aka fitar a cikin watanni tara na shekarar 2024, hukumomin ‘yan sanda

A Jamus, kyamar Musulmi na dada karuwa a kasar.

A wani rahoto da aka fitar a cikin watanni tara na shekarar 2024, hukumomin ‘yan sanda a Jamus sun ce mutane 42 da suka jikkata, ciki har da hudu masu tsanani, a duk fadin kasar, na da nasaba ne da kyamar Musulunci.

Sai dai wadannan alkaluma ba su da tabbas, domin a wasu lokuta ba a kai rahoton aikata laifuka kai tsaye ko kuma a lokacin bincike ne kawai ake gano dalilan dake da alaka da kyamar Musulunci.

A cikin rubu’i na uku na wannan shekara, an samu rahotannin laifuka 117, wanda ya nuna an samu raguwa idan aka kwatanta da kashi na biyu, inda aka samu laifuka 139.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments