Cibiyar “Khatamul-Anbiyaa”:  Iran Za Ta Mayar Da Martani Mai Tsanani  Idan Amurka Ta Kawo Wa Cibiyoyinta Hari

Mai Magana da yawun cibiyar rundunonin sojan Iran Ibrahim Zul-Fiqar ya gargadi Amurka da cewa, idan ku ka kawo wa muhimman cibiyoyinmu hari, to za

Mai Magana da yawun cibiyar rundunonin sojan Iran Ibrahim Zul-Fiqar ya gargadi Amurka da cewa, idan ku ka kawo wa muhimman cibiyoyinmu hari, to za mu kai hari akan cibiyin da su ka saura a cikin wannan yankin.

Zul-Fiqar ya kuma ce; Amurka mai danyen laifi tana ci gaba da nuna girman kai da kokarin girgiza zaman lafiya a cikin wannan yankin, muna kuma jaddada cewa ba za mu bari Amurkan da ta shigo wannan yankin daga waje ba, ta zama mai tsoma baki a harkokin mashigar wuwan Hurmuz ba.

Kakakin “Khatamul-Anbiyaa” ya kuma ce, batun mashigar Hurmuz, jan layin Iran ne wanda babu sako-sako akansa.

Zul-Fiqar ya ci gaba da cewa; Idan Amurkan ta aiwatar da barazanar da ta yi na kawo wa cibiyoyin Iran hari, to kuwa dukkanin cibiyoyin da su ka rage a wannan yankin za su fuskanci hari mai tsanani na sojojin jamhuriyar musulunci ta Iran, su zama toka. Haka nan kuma Zul Fiqar ya ce, Abokin gaba Jahili yana da masaniyar cewa; Lokacin gumurzu, ba abin gujewa ba ne a wurinmu, kuma abinda yake faruwa a yanzu shi ne mayar da martani mai tsanani, sannan anan gaba martanin zai fi haka tsanaki

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted