Ministococin harkokin wajen kasashen China da Iran sun tattauna kan halin da ake a yankin gabas ta tsakiya, da kuma yadda za su ci gaba da kara karfafa hadin gwiwa a tsakaninsu.
Kamfanin dillancin labaran IRNA ya bayar da rahoton cewa, Ministococin harkokin wajen kasashen China Wang Yi da na Iran Abbas Araghchi sun tattauna kan halin da ake a yankin gabas ta tsakiya, da kuma yadda za su ci gaba da kara karfafa hadin gwiwa a tsakaninsu a harkokin siyasa da diflomasiyya domin cin gajiyar juna.
A yayin ganawar tasu Araghchi ya yi wa takwaransa na China bayanin halin da ake ciki dangane da tattaunawar da ake yi tsakanin Iran da Amurka domin kawo karshen yakin da Amurka da Isra’ila suka kaddamar a kan kasar ta Iran.
A nasa bangaren ministan harkokin wajen China Wang Yi ya jaddada cewa, har kullum China tare da Iran, kuma harin da aka kaddamar a kanta ya sabawa dukkanin dokoki da ka’idoji na kasa da kasa, a kan haka ba za ta kasa a gwiwa ba wajen marawa Iran baya domin ganin an kawo karshen wannan rikici.