China Tayi Kira Da A Tabbatar Da Zaman Lafiya A Yankin

kasar china ta bukaci a tattabar da zaman lafiya a yankin kuma a kawo karshen yaki a yankin

Shugaban kasar china ji jinping yace china tana goyon bayan duk wani zaman lafiya mai dorewa a yankin yammacin asiya, ya jaddada cewa bai kamata yankin tekun fasha ya zama filin daga na gwada kwanji ga manyan kasashen duniya ba, adaidai lokacin da ake ganin yiyuwar amurka ta sake kaddamar da hare hare kan kasar iran

Shugaban na china ya yi wannan bayanin ne a lokacin ganawarsa da sarkin oman sarki haitham bin tariq al-said da ya kai ziyara a birnin baijin na kasar china a jiya litinin

Ministan harkokin wajen china yace bai kamata yankin ya zama wani dandamali na nuna karfin kasashe masu karfi na duniya ba,  yace zaman lafiya da tsaro a yankin na bukatar hadin guiwar dukkan bangarori wajen ciyar da su gaba da kuma karesu

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Rasha ta sanar a ranar litinin cewa babban jami’in musamman na kasar a yankin gabas ta tsakiya zhai jun zai ziyarci kasahen Iran oman da kuma kasar saudiya a wannan watan

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted