China Ta Kammala Gina Cibiyar Adana Bayanai Masu Amfani Da Karfin Iska

Kasar Sin ta kammala ginin wata cibiyar adana bayanai, irinta ta farko dake karkashin teku kuma mai amfani da lantarki daga karfin iska wato (UDC),

Kasar Sin ta kammala ginin wata cibiyar adana bayanai, irinta ta farko dake karkashin teku kuma mai amfani da lantarki daga karfin iska wato (UDC), wanda aka samar a birnin Shanghai na gabashin kasar. Cibiyar ta zama wani maunin inganci ta fuskar samar da kayayyakin sarrafa bayanai.

Cibiyar UDC wadda ke da mazauni a yankin Lingang na Shanghai, wanda yanki ne na kulla cinikayya cikin ‘yanci, ta samu jarin yuan biliyan 1.6, kwatankwacin kimanin dala miliyan 226, kuma tana da karfin lantarki da ya kai megawatt 24.

A cewar kwamitin gudanar da harkokin yankin Lingang, kammala aikin wata babbar nasara ce ga aikin samar da cibiyar UDC da kuma makamashi mai tsafta dake cikin teku. Ya kuma nuna yadda aka samar da wani tsarin sarrafa bayanai mai kare muhalli da kuma yadda kasar ke amfani da lantarkin da aka samar daga iska.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments