China: Al’ummar Syria Ne Za Su Ayyana Makomar Kasarsu

Ma’aikatar harkokin wajen kasar China ta bayyana cewa; Mutanen kasar ne ta Syria ya kamata su ayyana makomarsu, tare da yin kira ga dukkanin bangarori

Ma’aikatar harkokin wajen kasar China ta bayyana cewa; Mutanen kasar ne ta Syria ya kamata su ayyana makomarsu, tare da yin kira ga dukkanin bangarori da su yi amfani da hanyoyin siyasa domin tabbatar da tsaro da zaman lafiya a cikin kasar.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta China Mao Ning ta ce, kasar China taba bin diddigin abubuwan da suke faruwa a cikin kasar ta Syria, don haka tana fatan ganin cewa dukkanin mutanen kasar sun yi aiki domin kare manufofin al’ummar kasar na kusa da kuma nesa.

Tun a ranar 27 ga watan Nuwamba ne dai ‘yan ta’adda masu dauke da makamai da suke fada da gwamnatin Syria su ka fara kai hare-hare da zummar kifar da shugaba Basshar Asad da hakan ta tabbata a ranar Asabar din da ta gabata.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments