Kasar Chadi ta bukaci faransa da ta janye dakarunta daga kasar kafin ranar 31 ga watan janairun shekarar 2025 mai shirin kamawa.
Wannan na zuwa ne ‘yan kwanaki kadan bayan da gwamnatin Chadin ta sanar da kawo karshen yarjejeniyar hadin guiwa ta tsaro da kasar ta Faransa.
Bayanai sun ce bangarorin na ci gaba da tattaunawa a tsakaninsu game da shirin ficewar dakarun na faransa daga Chadi.
A makon da ya gabata dai Kasar Faransa ta fara janye sojojinta daga Chadi, inda ta fara janye wasu jiragen yakinta.
“Wannan shi ne matakin farko na maida kayan aikin Faransa da aka jibge a N’Djamena,” in ji shi, kuma ajandar ficewar zai dauki makonni da yawa kafin a kammala.
Vernet ya jaddada cewa, ana ci gaba da tattaunawa da jami’an kasar Chadi dangane da lokaci da kuma hanyar da Faransa za ta janye sauran dakarunta 1,000 a kasar ta Afirka, da kuma ko dukkansu za su fice.
Kasar Chadi ta kasance kawa ga Faransa a yakin da ake yi da ta’addanci, kuma daya daga cikin kasashen karshe da Faransa ta girke sojoji a yankin, bayan da aka kore su daga kasashen Nijar, Mali da Burkina Faso.
A wani mataki na ba-zata da gwamnatin kasar Chadi ta dauka a ranar 28 ga watan Nuwamba, ne ta sanar da kawo karshen yarjejeniyar tsaro da ta kulla da Faransa, inda ta bayyana hakan a matsayin wani sauyi ga kasar tare da jaddada cewa, matakin zai bai wa kasashen Afirka damar sake daidaita huldar abokantaka daidai da manufofin kasashensu.