Tawagar ‘yan wasan kwallon kafa na ‘yan kasa da shekara 20 ta Afrika ta Kudu ta lashe kofin gasar CAN a karon farko bayan da ta doke takwararta ta Morocco (1-0) a wasan karshe da aka buga a birnin Alkahira jiya Lahadi.
Kafin hakan Najeriya ta samu matsayi na uku a gasar bayan da ta doke Masar mai masaukin baki a bugun fenariti (1-1; 4-1 a bugun fenariti).
Kasashen guda hudu da suka fafata a wasan kusa da na karshe wato (Afirka ta Kudu, Morocco, Najeriya, Masar) sun samu tikitin shiga gasar cin kofin duniya na ‘yan kasa da shekaru 20 a kasar Chile da za’a gudanar daga ranar 27 ga Satumba zuwa 19 ga Oktoba, 2025.