Mutane kimani 60 ne zasu gurfana a gaban kotu a kasar Burtaniya, saboda goyin bayan kungiyar mai goyon bayan Falasdinu, wata :frre Palastine’ wacce kuma gwamnatin ta bayyanata a matsayin kungiyar yar ta’adda.
Labarin ya kara da cewa wannan shi ne zanga zangar da aka fi kama mutane tun lokacinda aka fara zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa a shekara ta 2023.
Masu goyon bayan Falasdinawa 3 wadanda aka kama a cikin watan Julin da ya gabata, an rika na gabatar da su a gaban kotu kuma kuma za’a tuhumesu karkashin doka da “Yan ta’adda na kasar.
Yansanda sun bayyana cewa kotu tana iya yanke hukuncin zaman gidan kaso har na tsawon watanni 6 a kan ko wanne daga cikinsu.
A jiya jumma’a ce majiyar yansada na birnin London na cewa: tunda a wannan karon sun kama mutane da yawa, wato mutum har 60, to suna iya rarrabasu zuwa gungu-gungu don gabatar da su a gaban kotu karshen dokar nan ‘wacce suke kira ayyukan ta’addanci.
Labarin ya kara da cewa Jam;iyyar Labour ce ta bukaci a sanya kungiyar ‘Action for Palastine, a matsayin kungiyar yan ta’adda.
Kungiyar dai ta saba shirya zanga-zanga a karshen ko wani mako inda dubban mutane sukan shiga don yin Alla wadai da HKI kan kissan kiyashin da take aikatawa a Gaza.