Bukhaiti: HKI Ta Ketari Jan Layimmu, Ta Jira Maida Martanimmu

Mamba a majalisar gudanarwa ta kungiyar Ansarulla ta kasar yemen Muhammad Bukhaiti ya bayyana cewa hare-haren da HKI da Amurka suka kai fararen hula a

Mamba a majalisar gudanarwa ta kungiyar Ansarulla ta kasar yemen Muhammad Bukhaiti ya bayyana cewa hare-haren da HKI da Amurka suka kai fararen hula a kasar yemen wuce jan layi, ko ketare haddi ne na kungiyar don haka su jira maida martani mai tsanani.

Kamfanin dillancin labaran Iran ya nakalti yana fadawa tsahar talabijin ta Al-mayadeen ta kasar Lenamon a yau Talata.  Ya kuma kara da cewa hare-haren da Amurka suke kaiwa ma’aikatu da wuraren fararen hula a kasar Yemen na baya-bayan nan duk sun nuna cewa an sami nasara a kansu.

Albukhaiti ya kara da cewa sadaukarwa da mutanen kasar Yemen suke yi saboda Gaza, ba zai tsaya ba, sannan muna son fadawa kasashen Amurka da ingila da kuma HKI kan cewa su ji maida martanimmu.  Ya kuma kara da cewa, hare-haren da suka kaiwa ma’aikatu da kuma wuraren fararen hula a kasar Yemen ba zai yi wani tasiri a cikin goyon bayan da muke yiwa mutanen Gaza ba. Yace kasar Yemen a shirya take ta fuskance dukkan bangarorin guda 3.

A safiyar yau Talata ce jiragen yakin HKI suka kai hare-hare kan tashar jiragen sama na Sa’a inda suka kai mata hare-hare har guda 15. Sammam labarin ya kara da cewa jiragen yakin HKI kimani 30 suka yi wammam aikin.  

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments