Brazil Ta Goyi Bayan Iran Kan Hakkinta Na Mallakar Makamashin Nukiliya

Kasar Brazil ta jaddada goyon bayanta ga ‘yancin Jamhuriyar Musulunci ta Iran na amfani da makamashin nukiliya na zaman lafiya A yayin ganawarsa da sakataren

Kasar Brazil ta jaddada goyon bayanta ga ‘yancin Jamhuriyar Musulunci ta Iran na amfani da makamashin nukiliya na zaman lafiya

A yayin ganawarsa da sakataren kwamitin kolin tsaron kasar Iran, mataimaki na musamman ga shugaban kasar Brazil ya sanar da cewa kasarsa tana goyon bayan ‘yancin Jamhuriyar Musulunci ta Iran na yin amfani da makamashin nukiliya na zaman lafiya da kuma aiwatar da shirin inganta sinadarin Uranium don bunkasa harkokin ilimi cikin gida ta hanyar fasahar makamashin nukiliya.

A yayin ganawar tasu, Ali Akbar Ahmadian, sakataren majalisar kolin tsaron kasar Iran, da mataimaki na musamman ga shugaban kasar Brazil Celso Amorim, sun jaddada muhimmancin ci gaba da gudanar da hadin gwiwa da tuntubar juna tsakanin kasashen biyu masu cin gashin kansu, don tunkarar manufofin bai daya.

Har ila yau Ahmadian ya yi Allah wadai da laifukan gwamnatin yahudawan sahayoniyya a Gaza tare da jaddada wajabcin hadin kai tsakanin kasashe da al’ummomi da ke adawa da mulkin mallaka wajen tunkarar gwamnatin mamayar ‘yan sahayoniyya. Ya kuma jaddada cewa, bai kamata duniya ta yi shiru ba dangane da bala’in jin kai da ake ci gaba da fuskanta a zirin Gaza, yana mai kira da a hada kai wajen tunkarar masu aikata wannan ta’asa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments