Bokoharam Ta Kashe Sojojin Kamaru Ta Hanyar Amfani Da Jirgin Sama Maras Matuki

Majiyar tsaron kasar ta Kamaru sanar da cewa, da dama daga cikin sojojin kasar sun rasa rayukansu sanadiyyar wani hari da kungiyar Bokoharam ta kai

Majiyar tsaron kasar ta Kamaru sanar da cewa, da dama daga cikin sojojin kasar sun rasa rayukansu sanadiyyar wani hari da kungiyar Bokoharam ta kai musu ta hanyar amfani da manyan bindigogi da kuma jirgin sama maras matuki akan iyaka da Najeriya.

Majiyar ta ce an kai harin ne a yankin Sagami dake kusa da tafkin Chadi a gundumar Logun mai iyaka da kasar Najeriya.

Ita dai kungiyar Bokoharam ta addabi kasashen Najeriya, Kamaru da kuma jamhuriyar Nijar. Yankun arewacin kasar ta Kamaru ya fara fuskantar kai hare-hare daga wannan kungiyar ne tun a 2014 wanda kuma har yanzu yana ci gaba da faruwa daga lokaci zuwa lokaci.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments