Shugaban mabiya darikar Katolika na duniya Fafaroma Francis, ya yi kira da a tsagaita wuta a Gaza.
A cikin sakonsa na bikin Easter, Paparoma ya yi tir da halin da ake ciki na jin kai a Gaza tare da yin kira da a tsagaita wuta.
Paparoma Francis ya halarci bukukuwan Ista a wannan Lahadi, inda ya yi tir da halin da ake ciki na jin kai mai daukan hankali a Gaza.
“Ina kira ga bagarorin da su tsagaita wuta, a saki wadanda aka yi garkuwa da su, a kuma kai kayan agaji ga al’ummar falasdinu da kuma fatan samun zaman lafiya a nan gaba,” in ji shi a cikin sakonsa, wanda wani na hanun damansa ya karanto daga cocin St. Peter’s Basilica dake binrin Rome.
Jawabin nasa wani bangare ne na bikin Easter kamar yakke ake a ko wacce shekara, saidai fafaroman bai samu karanto jawabinba sabo lalurar ta rashin lafiya da yake fama da ita.
Mabiya addinin Kirisita a fadin duniya kan gudanar da bukukuwan Easter duk shekara domin tunawa da gicciyewa da kuma tashin Yesu Almasihu daga cikin matattu.
Bikin dai a kan fara shi ne tun daga dare irin na Alhamis zuwa wayewar garin Juma’a a kuma kammala a ranar Litinin.