Ben Gafir Ya Bukaci Gwamnatin HKI Ta Mamaye Yankin Gaza Gaba daya

Ministan tsaron cikin gida na HKI Itamar Ben-Gvir ya yi kira ga babban murya kan cewa dole ne HKI ta mamaye dukka zirin gaza ta

Ministan tsaron cikin gida na HKI Itamar Ben-Gvir ya yi kira ga babban murya kan cewa dole ne HKI ta mamaye dukka zirin gaza ta kuma kori falasdinawa da suke cikinsa.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalato Ben Gafir yana fadar haka a jiya ya kuma kara da cewa mamaye gaza da kuma yankin yamma da kogin Jordan da kuma shi ne kawai zai sa a samar da kasar yahudawan zalla inda babu ba falasdine ko guda a yankunan guda biyu.

Kiran nasa dai ya gamu da maida martani daga yan siyasa a ciki da wajen HKI.

Tun shekara ta 2023 ne gwamnatin HKI take son mamyar zirin gaza ta kuma kori Falasdiwa a yankin. Bayan yaklin da kungiyar Hamas ta fara a ranar 7 ga watan Octoban shekara ta 2023

Amma da alamun yahudawan sun kasa, saboda har yanzunn kungiyar Hamas tan gaza kuma tana ci gaba da halaka sojojin yahudawan a cikinsa.

A halin yanzu dai yahudawan sun kashe falasdinawa fiye da dubu 50, kuma suna ci gaba da kashesu a duk ranar All.. musamman a wajen tarkon karban abinci da suka kafa masu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted